Gwamnatin Kaduna ta kori ma’aikatan kananan hukumomi sama da 4000

0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da Koran ma’aikatan kananan hukumomi sama da 4000 dake fadin jihar.

Kwamishinan kananan hukumomi da raya masarautu na Kaduna, Jafaru Sani ya ce gwamnati ta yi haka ne domin inganta ayyukan kananan hukumomin jihar.

Ma’aikata 4,042 wannan garambawul ya shafa, inda ma’aikata 3,159 da suka kai shekara 10 suna aiki aka yi musu ritaya, sauran 893 kuma aka sallama. Bayan haka kuma ja’afaru ya ce za a biya hakkokin wadanda abin ya shafa. Ya kara da cewa za a biya su duka albashin watan Nuwamba da kuma kudin sallama.

” Yanzu jihar Kaduna na da ma’aikata 6,732 da ke aiki a kananan hukumomin ta banda malaman makarantun Firamare da ma’aikatan kiwon lafiya.

Share.

game da Author