HARKALLAR NAIRA BILIYAN 1: Yeriman Bakura ya kusa sanin makomar sa

1

Ranar 5 Ga Disamba ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani zai san makomar sa dangane da zargin da ake yi masa na yin harkallar naira biliyan daya.

Yerima, wanda a yanzu sanata ne, ya na fuskantar tuhuma ta laifin karkatar da makudan kudaden a lokacin da ya ke gwamnan jihar Zamfara.

Shi ne gwamnan da ya fara kaddamar da shari’ar musulun ci, har aka yanke wa wani haddin datse masa hannu a jihar.

Hukumar hana cin hanci da rashawa, ICPC ce ta gurfanar da shi, a gaban Mai Shari’a Bello Gummi a Babbar Kotun Jihar Zamfara da a ranar Juma’a.

Mai gabatar da kara, Christiana Onougu, ta gabatar da masu shaida har mutum shida, sannan ta mika kotun wasu takardun shaidu har 25, tare da cewa ta kammala binciken ta. Shi kuma lauyan da ke kare Yerima, ya gabatar da shaidu guda shida.

Mai gabatar da kara Onougu ta ce shaidun da ta mika wa kotu, sun isa su tabbatar da cewa Sanata Yerima ya karkatar da wadannan kudade naira bilyan daya da aka karba bashi daga bankin UBA.

Share.

game da Author