2019: Wata kungiya ta ce “Sai Atiku”

0

Wata kunguya mai suna CC4A, wato masu kaunar Atiku ya fito takara, sun bayyana cewa su na goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya fito takarar zaben shugaban kasa a 2019.

Duk da cewa har yanzu Atiku bai fito ya bayyana cewa zai tsaya takara ba, kungiyar ta nemi ya gaggauta fitowa ya nuna bukatar sa ta fitowa takara. Shugaban kungiyar Adebowale Jante ne ya bayyana haka a wata ziyara da su ka kai ofishin lada labaran Atiku da ke Jabi, Abuja.

Daraktan yada labaran ofishin Paul Ibe shi ne ya karbi ’yan kungiyar, inda ya nanata musu cewa Najeriya na gaggawar bukatar shugaba wanda ya cancanci jagorantar kasar, kamar Atiku Abubakar. Ya na mai kara cewa wannan ziyara za ta kara zaburar da Atiku, musamman ma a wannan yanayi da ake ciki na rashin kwararan shugabanni.

Daga nan sai ya jaddada wa matasan kada guyawun su su sare wajen kokarin da suke yi ganain an samu shugaba mai hangen-nesa kamar Atiku.

“Ran ka ya dade, muna alfahari da ka bu damar kawo maka wannan ziyara, domin kungiyar mu ta matasa ce masu kishin Najeriya a jini da zuci ba da baki kawai ba. Muna da muradin ganin an gaggauta hawa tudu-mun-tsira a fannin tattalin arzikin mu.

“Kungiyar mu ta na da rassa a dukkan fadin jihohin mu 36, da kuma wasu kasashe a duniya.

Jante ya kara da cewa sun yi nisa wajen sjirye-shiryen ganin Atiku ya fito takara, domin yanzu sun ma wuce matakin rokon Wazirin na Adamawa ya fito, ya ce ai ya ma zama tilas Atiku ya fito takara a 2019 domin a gaggauta ceto Najeriya.

Share.

game da Author