Dalilan da ya sa aka umarci sojojin Najeriya koyon Hausa, Yarbanci da Ibo

0

Hukumar Sojojin Kasar nan ta bada sanarwar cewa kowane soja ya tabbatar ya koyi yaren Hausa, Yarbanci da kuma Ibo kafin nan da 2019.

Kakakin Sojoji Sani Usman ne ya bayyana haka a ranar Laraba ta yau, inda ya ce ana bukarar sojojin su koyi yarukan guda uku nan da karshen Disamba, 2018.

Burgediya Janar Usman ya ce wannan umarni da aka ba sojojin ya na daga cikin wasu sabbin tsare-tsare da sojoji suka shogo da shi.

DALILAN BADA UMARNIN A KOYI HAUSA, IBO DA YARABANCI

1. Rundunar Jojojin Najeriya ta shigo da tsarin koyon wasu yarukan kasashen ketare da kuma na nan gida Najeriya domin a haka domin a saukaka tafiyar da sakonni a tsakanin juna, samowa da binciko bayanai, gyara hulda a tsakanin sojoji da farar hula sai kuma kara taimaka wa karabiti da manyan sojoji gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

2. Amma fa a sani har yanzu Turanci ne takamaimen yaren hukumar. Sai dai su yarukan na cikin gida za a rika amfanin da su yayin da ake wasu farmaki, sintiri ko kuma yin tambayoyi ga wasu masu laifi. Har kudin alawus ma za a rika bayarwa ga wadanda suka koyi magana da yarukan.

3. Ga masu son shiga aikin soja, koyon wadannan yarukan zai zama hanya mai saurin a dauke shi aiki.

4. Kafin wannan sanarwa, yarukan da sojoji ke amfani da su, sun hada da French, Arabic, Spanish, Portuguese da Swahili.

Share.

game da Author