Majalisar Dattawa ta dage zaman nazarin kasafin kudin 2018

0

Majalisar Dattawa ta dage zaman da ta shirya yi domin tattauna kasafin 2018, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar makonni biyu da suka gabata.

Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya ce za a fara zaman a ranar 28 Ga Nuwamba din nan.

Saraki ya ce dage zaman ya zama wajibi ne saboda saboda tsaiko ko lattin da aka samu a bangaren Rahoton Shirin MTEF wanda gwamnati ke kiyasin abin da za ta kashe tsakanin 2018 zuwa 2020.

Share.

game da Author