An kashe mata da yara sama da 60 a harin Adamawa, inji Miyetti Allah

0

A kalla yara da mata 30 ne suka rasa rayukansu a harin da wasu mahara suka kai ranar Litini a kauyukan dake karaman hukumar Numan jihar Adamawa.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da aka kai wa hari, Oriwa Hammadu ya ce maharan manoman Bachama ne suka kai wa Fulanin dake kauyukan Shafaran, Shawal, Gumara, Kikam da Kadamti hari.

” Manoman Bachama sai da suka bari duk mazan kayukan sun tafi balaguron su sannan suka far wa matan mu da yaran mu.”

“Mun iya gane maharan ne ta wakar da suke ta rerawa na yaki da harshen yaren Bachama.”

Ya ce an kai gawawwakin wadanda suka rasu da wadanda suka sami rauni a harin asibitin dake Numan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Othman Abubakar ya ce mata da yara Fulani 30 ne aka kashe a wannan hari.

Ya ce sun fara gudanar da bincike don ganin sun kama maharan musamman yadda suka sami labarin cewa maharan manoman Bachama ne.

Bayan haka a safiyar Laraba ne gwamnan jihar Adamawa Jibirilla Bindow ya ce gwamnati za ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan wannan hari da aka kai kauyukan da kumayayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 60.

Kungiyar Miyetti Allah tace zuwa yanzu, gawa 60 ne suka irga.

Share.

game da Author