BAKON DAURO: Mutane 15 sun mutu a jihar Gombe

0

Wani jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO Raymond Dankoli yace mutane 15 daga cikin 864 da ake zargin sun kamu da cutar bakon dauro jihar Gombe sun mutu.

Ya sanar da haka ne a taron da cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na jihar ta shirya ranar Alhamis kan wayar da kan mutane mahimmancin yin rigakafin cutar karanbau da za su fara ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 15 ga watan Disemba.

Ya ce bana kananan hukumomi 7 ne a jihar suka kamu da cutar inda karamar hukumar Gombe ta fi yawan mutanen da suka kamu.

Dankoli ya ce jihar ta dauki matakan shawo kan yaduwar cutar ta hanyar samar da isassun magungunan kawar da cutar tare da kwararrun ma’aikatan da za su gudanar da bincike kan bullowar cutar.

Ya ce bana za su yi wa yara ‘yan watanni 59 alluran rigakafin cutar bakon dauro sannan suna sa ran yi wa kowani yaro alluran rigakafin cutar koda ko ya riga ya yi rigakafin kafin wannan lokacin da za su fara.

Bayan haka shugaban fannin bada alluran rigakafi na cibiyar kiwon lafiya na matakin farko Musa Kuna ya ce suna kokarin gano dalilin da ya hana mutane fitowa da yaran su domin yin alluran rigakafi a shekaran 2015.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar sun adana katin yiwa ‘ya’yan su alluran rigakafi domin katin ne za su yi amfani da shi wajen sanin yawan yaran da suka yi wa alluran.

Share.

game da Author