Abubuwa 5 da El-Rufai zai yi da bashin dala miliyan 350

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I yace jihar na so ta karbo bashin dala miliyan 350 daga bankin duniyar don ta iya cin ma burin ta na samar wa mutanen jihar ababen more rayuwa kamar yadda ta yi alkawari a lokacin kamfen din 2015.

1. Jihar za ta yi amfami da kudin ne wajen samar da kayan aiki a makarantun gwamnati a jihar musamman wadanda ke fama da matsalolin rashin runfuna, kujerun zama, kofofi, tagogi, ban dakuna, ruwa da ofisoshin malamai.

2. Gwamnati za tayi amfani da kudin wajen gina karin Ajujuwa da sabbin makarantu domin karin yara da ake samu wadeanda ke so su shiga makarantun jihar da kuma wadanda ke ciki su sami walwala.

3. Za kuma su yi amfani da kudin wajen samar da kayan aiki a manyan asibitoci 25 da cibiyoyin kiwon lafiya 255 dake jihar.

4. Gwamnati za tayi amfani da kudin wajen gyara manya da kananan tituna dake jihar.

5. Bashin kudin zai taimaka wajen kammala aikin samar da ruwan sha da gwamnati ke yi a yanzu haka a duka fadin jihar.

Share.

game da Author