KANJAMAU: Wata ‘yar shekara takwas ta rasu a sansanin Dalori

0

Mazauna sansanin Dalori II a jihar Barno suna zaman juyayi sanadiyyar rasuwar wata yarinya ‘yar shekaru 8 a sansanin da ta kamu da cutar Kanjamau.

Bisa ga bayanan da wasu mazaunan sansanin suka bada cewa yarinya mai suna Bana-Losoraye ta rasu ne.

Mahaifinta ya dade da rasuwa, shima ya kamu da cutar ne kafin Allah yayi masa cikawa.

Malama Aishatu dake kula da marigayiyar ta sanar wa PREMIUM TIMES cewa Bana-Losoraye ta zo sansanin Dalori II tare da mahaifiyarta da kakanta daga kauyen Banki wanda ke kusa da bodar Kamaru.

Fatima wanda ita ma tana zaune ne a wannan sansani na Dalori ta ce ko da suka zo sansanin, an gudu ne ba a tsira ba domin basu sami kulan da suke bukata ba wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mahafiyar Bana-Losoroye sannan kakan ta rasu bayan wata daya da rasuwar mahaifiyar ta.

Kwamishinan kiwon lafiyan jihar Borno Haruna Mshelia ya ce tabarbarewan rashin lafiyar Bano-Losoroye na da nasaba da yadda masu kula da yara ke boye cutar dake tattare da yaran. Mai makon su sanar likitoci halin da suke ciki sai su boye abin har sai tayi musu illa.

“Mai yiwuwa ne matan dake kula da marigayiyar sun boye cutar da take dauke dashi har sai da ya kar ta kafin akai ta asibiti.”

Ya ce an kafa wurare da dama da masu dauke da cutar kanjamau musamman mata masu juna biyu za su dunga samun kulan da suke bukata amma saboda hali na ko-in-kula ba za su zo su karban magani ba sai malaman asibiti sun biyo su har daki sun tilasta musu kafin su sha magtanin.

Share.

game da Author