Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa har yanzu akwai wasu kauyuka da ke kashe tagwaye, wato ‘yan biyu idan har daya daga cikin su ya haifa a Abuja.
Kauyukan da ke aikata wannan mummunar abu kuwa sun hada da Basa Komo, Chukuku, Gaube, Chibiri, Kulo, Kiyi, Gawu da Sabo, da wasu a yankin Kwali da ya hada da Dogon Ruwa, Fuka, Gomani, Lapa, Gurugi, Sadaba, Kwala da Keru.
Idan ba a manta ba tarihi ya nuna cewa wata baturiya ce mai suna Mary Slessor ta hana wannan mummunar al’ada garin Calabar, babban birnin jihar Cross-Rivers a yanzu inda ada da zaran mace ta haifi ‘yan biyu sai su dauke su su saka su a cikin tukunyar kasa sannan su jefar dasu a gungurmin daji.
Amma sai gashi wadannan kauyuka da muka ambato dake babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja na aikata irin haka duk da waye da aka samu da ci gaba.
Bayan haka an gano cewa, irin wannan al’ada na kashe ‘yan biyu bai tsaya a nan ba kawai, har ‘yan uku, ‘yan hudu, ‘yan biyar da yaran da suka zo duniya dauke da wani cuta ko masakai.
Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan, Zaka Musa ya ce har yanzu akwai gidajen dake aikata haka amma a boye batare da sanin masu unguwanin kauyukan ba. Sai dai kuma da aka zanta da wasu masu unguwanni dake wadannan kauyuka suna ce basu da masaniya cewa hakan na faruwa a wadannan kauyuka.
Bayan haka shugaban wani gidan marayu dake garin Kuje ‘Vine Heritage Home’, Stephen Olusola ya koka kan yadda wadannan mutane suke aikata wannan abu har yanzu. Ya ce ya gamu da irin wadannan mutane da har yanzu suke aikata hakan a wa’azin yada addinin kirista da yake yi.
“Akwai wani kauye da ake kira gidan Gbajingala dake Basa Komo da har yanzu suna aikata irin wannan abu. Sannan Kuma suna kashe marayu yara da iyayen ke rasuwa su bar su, da kuma yara irin wadanda ake haihuwa da wani lahani a jikin su, musakai.
A nasu ganin irin wadannan yaran basu cancanci a barsu su rayuba.
Daga karshen yayi kira ga gwamnati da malaman addini da su karkata akalar su zuwa irin wadannan kauyuka domin wayar musu da kai da nuna musu illar abin da su keyi.