Kamfanin Intels mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya mayar wa gwamnatin tarayya kakkausan martani, dangane da soke yarjejeniyar kwangilar shekaru 17 da gwamnatin baya ta ba kamfanin.
A yarjejeniyar da aka yi da Intel tun shekarar 2010, an rattaba hannu cewa Intels ne zai rika karbar kudaden haraji daga manyar jirajen ruwa masu kwasa da sauke lodi a tashoshin kasar nan.
Sai dai kuma bayan hawan gwamnatin APC, gwamnatin da Atiku ya taka muhimmiyar rawar kafuwar ta da samun nasarar ta, sai aka fara tunaninn yadda za a soke wannan kwangila da Intels ke yi.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya rubuta wa Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala cewa ta soke kwangilar ta dala miliyan 70 duk shekara, a bisa hujjar cewa ta saba wa doka ta sashe na 8(1) da kuma na 162(1).
An dai bai wa Intels wannan kwangila ce tun cikin 2010, wanda a ranar 27 Ga Satumba, 2017, Malami ya ce a soke ta bayan an kwashe shekaru bakwai ana gudanar da ita.
Kamfanin Intels ya maida zazzafan martani a jiya Laraba, ya na mai shaida wa gwamnatin Najeriya cewa soke kwangilar dungurugum da aka yi ranar Talata, 10 Ga Oktoba, 2017, “sakarci ne, shashanci ne, wauta ce kuma abin dariya ne.”
Intels ya kara da cewa soke wannan kwangila zai yi wa Najeriya mummunar illa.
Shugaban Intels, wanda shi da Atiku ne suka hada guiwa su ka kafa kafa kamfanin, ya rubuta wa Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya wadda ta soke kwangilar cewa a fa tuna makudan kudaden da Intels ya narkar wajen narkar da jari da kaddarorin sa a tashar jiragen ruwa ta Badagry, a Legas, zai samar wa dubban ‘yan Najeriya ayyukan yi.
Silvano Bellinato, ya ci gaba da bayyana cewa Intels ya narka makudan kudade a kasa wajen kafa kamfanin sa domin tafiyar da ayyukan kwangilar da aka yi yarjejeniya tun cikin 2010 kuma aka ci gaba da ayyuka.
“Don haka idan wata gwamnati a yanzu bayan shekaru bakwai za ta fito da rana tsaka ta soke kwangilar ba tare da bin ka’idoji da sharuddan soke kwangilar ba, to za mu kau da kai mu kai kara kotu, mu ga wanda zai yi nasara.”
Daga nan sai kamfanin ya ba Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, NPA kwanaki bakwai da ta janye soke kwangilar a sake duba yadda bangarorin biyu za su cimma maslaha, ko kuma ta rankaya kotu, domin a ba mai gaskiya gaskiyar sa.
Intels ya ce kekasa kasar da NPA ya yi wajen yin biris da duba koken da Intels ya isar masa, shi ya sa ake neman a yi wa Intels karfa-karfa.
“Ita kan ta Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta amince da cewa Intels na bin ta dimbin bashi har na Dala Miliyan 674,767,415.00. Sannan kuma sai a hada da kudin ruwan da ke kan bashin saboda dadewar da aka yi ba a biya ba.”
‘Don haka mu na kira ga NPA da su bi ka’idar yarjejiyar kwangila mai lamba 13, wadda aka rattaba tsakanin Hukumar da Intels tun 2010, nan da kwanaki 7 su shirya zaman neman sulhu domin neman yadda za a warware matsalar cikin sulhu.
“Idan ba haka ba kuwa, to mu na sanar da ku kamar yadda dokar yarjejeniya ta 13 ta ce mu sanar da ku, cewa, za mu bi hanyar da ta dace domin mu kare kamfanin mu daga dibga babbar asarar da ku ke neman haifar mana. Wannan hanya kuwa ita ce ta daukar mataki na shari’a da ku.”