A ranar lahadi ne fadar shugaban kasa ta sanar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ta karbi kudaden da ya kai Naira biliyan 1.2 tsakanin shekarun 2015 da 2017.
Mataimakin darektan yada labarai Attah Esa ya sanar da haka.
Ya ce idan ba a manta ba a kwanakin da suka gabata ne hukumar asibitin ta ce za ta mai da asibitin hannun ‘yan kasuwa saboda karancin kudi da take fama da shi.
Jin irin wannan makudan kudaden da hukumar asibitin ta karba ne ya sa wasu ‘yan Najeriya kamar matar shugaban kasa Aisha Buhari ta kushe aiyukkan asibitin inda ta ce ‘‘Ina amfanin duk yawan kudaden da suke karba daga gwamantin tarayya sannan asibitin na fama da karancin kayan aiki?”
Bayan haka Attah Esa bisa ga bayanan da shugaban asibitin Jalal Alabi ya ce hukumar asibitin ba ta karbi kudaden da ake cewa ta karba daga gwamanti ba.
” A tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 mun karbi kashi 33 bisa 100 na kudaden da muke bukata domin gudanar da wasu manyan ayyukan mu da kuma kashi 48 bisa 100 na kudaden da muke bukata wajen gudanar da aiyukkan mu na yau da kullun kadai’’.
‘‘ A shekaran 2017 mun karbi kashi 27.54 bisa 100 ne kawai.”
Attah Esa yace za a iya samun tabbacin hakan wajen ma’aikatan kudi, kasafi da shirye –shiryen na kasa.
Daga karshe ya kuma ce hakan bai hana su gudanar da aiyukkan su da ya kamata ba wanda ya hada da kula da lafiyar ma’aikatan gwamnati da sauran mutane.