Dangote zai dauki masu digiri domin aikin noman shinkafa

0

Kamfanin Noman Shinkafa na Dangote Rice Limited da ke jihar Kogi, zai dauki matasan da suka kammala jami’a domin aikin noman shinkafa.

Wannan shiri ya zo ne yayin da kamfanin ya sha alwashin noma shinkafa kimanin metric ton har miliyan daya a cikin 2018.

An kafa wannan aikin noma ne domin samar wa matasa aikin yi, wanda aka fara a gabar Kogin Neja da ke Kampe, cikin karamar hukumar Yabga ta Yamma, a cikin jihar Kogi. Ana kuma noma har hekta 100 ce.

A wannan tsarin dai matasan ne za su noma shinkafar yayin da kamfanin zai saya ya cashe ta da kan sa.

Kamfanin Dangote ne zai bai wa matasan irin shinkafar da za su shuka, ya ba su maganin kwari, ya ba su taki, yayin da hukumar noman rani ta River Niger za ta bayar da filayen noma.

Share.

game da Author