‘Yan siyasan Kudu Maso Gabas ne ke tunzura mutane – Rundunar Soji

0

Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya ce ‘Yan Siyasar yankin Kudu Maso Gabas ne ke tunzura mutane yin sa-in-sa da sojoji.

” Abin takaici ne yadda wasu yan siyasa ke yin amfani da abubuwan da ke faru domin tunzura mutanen gari da Sojojin Najeriya a kasar nan.

Ya ce atisayin da sojoji ke yi a garin Aba ya kama ne amma ba wai don su takura wa jama’a ba. Sannan zasu gudanar da irin wannan atisayi a yanki Kudu maso Yamma.

Yayi kira ga jama’a da su ba sojojin hadin kai sannan su tabbata sun bi doka.

Share.

game da Author