Shugaban karamar hukumar Bagudo jihar Kebbi Muhammad Zagga ya ce mutane 53 ne suka rasa rayukansu a wata hadarin jirgin ruwa da aka yi a garin.
Muhammed Zagga ya ce jirgin ruwan da ke dauke da ‘yan kasuwa da suka kai 100 ya kife ne yayin da suke hanyar su na zuwa kasuwan Lolo.
Ya ce an tsamo mutane 47 daga cikinsu.
“Mafi yawan fasinjojin dake cikin jirgin ruwan ‘yan kasuwa ne daga jamhuriyar Nijar.”
Muhammed Zagga ya ce mutanen 500 wanda suka kware a nitso na nan na neman sauran mutane 53 da ba a gansu ba.