Kungiyar Jama’atu ta umurci limaman karsar nan da su kwadaitar da mutane kan zaman lafiya a ko-ina suke a kasar nan a hudubar su na ranar Juma’a.
Sakataren kungiyar jama’atu Dr Khaleed Aliyu ne ya fadi haka a Kaduna da yake zantawa da manema labarai.
” Kungiyar JNI ta yi haka ne don a kwantar da hankalin mutane da horan su da zaman lafiya a tsakanin juna.”
” Ganin cewa kungiyar JNI cikin jagorancin sarkin Musulmi, na da iko akan kungiyoyin mususlunci a kasar nan ne ya sa tayi wannan kira don kada a tada hankula a jihohin mu.”
Bayan haka kungiyar ta yi kira ga shugabannin yankin kudu maso Gabas da su yi kira ga matsan yankin da su kwantar da hankulansu su dai na neman tada zaune tsaye.