Limamin Alfurkan, Kano yayi kira da a zauna lafiya da Juna

0

Limamin masallacin Juma’a na Alfurqan dake garin Kano Bashir Umar ya yi kira ga musulmai da su guji daukan fansa kan mutane musamman wadanda ba adinin su daya ba.

Ya fadi haka ne a hudubar sa na sallar Juma’a in da ya yi da kada a ce za a dauki fansa kan abubuwan da yake faruwa a yankin kudu maso gabas.

Ya ce adinin musulunci na karantar da zaman lafiya ne ba tashin hankali ba.

Share.

game da Author