Mun fara shirye-shiryen Hajjin badi – Shugaban NAHCON, Abdullahi Mukhtar

0

Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta ce ta fara shirye-shiryen hajin badi tun yanzu.

Shugaban hukumar Abdullahi Mohammed ne ya sanar da haka a taron wayar da kai da duba yadda ayyukan a bana suka gudana da hukumar tayi a garin Makkah.

Ya ce sun fara wannan shirin domin su inganta aikin a shekara mai zuwa ta inda mahajjata za su samu masauki masu kyau sannan kusa da harami. Ya kara da cewa yin hakan zai sa a sami rangwamen kudin kujera a badi.

“Muna fatan za mu sami nasarar cimma wannan buri na mu da muka sa a gaba a 2018.”

Bayan haka Abdullahi Mohammed ya yi kira ga yan jarida da ke dauko rahotanni daga kasar lokacin aikin hajji da su dinga nuna kwarewa a aikinsu domin wasu labaran da suke aikawa dasu ba su kai a fitar ba ko kuma ba ayi binciken da ya kamata ba kafina fitar.

Ya koka da wani rahoto da wani dan jarida ya fitar na wani barawo da wai kukumomin Saudi sun daure shi saboda aikata laifin sata da yayi cewa ba haka.

“Wani ma’aikacin jarida ya rubuta labarin wani mahajjacin da aka daure na tsawon watan uku don ya tsinci jaka a masallacin manzon Allah (SAW) ba tare ya tabbatar da inganci labarain ba. Inda daga baya abin ya zamo ba haka bane.”

Ya ce ba a yanke wa mahajjacin wannan hukuncin ba sannan lauyoyinsu na nan akan maganan.

Share.

game da Author