Yadda Gwamnoni Kudu-maso-Gabas suka haramta Kungiyar IPOB

0

Jim kadan bayan kammala taron su a yammacin Alhamis, a fadar Gwamnatin Jihar Anambra, Gwamnonin Kudu-maso-kudu sun haramta kungiyar IPOB masu hankoron kafa Biafra.

Ga sakamakon taron:

1. An soke duk wasu ayyukan Kungiyar Neman Kafa Biafra. Ko ma wa ke da wani korafi musammam kan abin da ya shafi kasar nan, to ya mika kukan sa ga Kwamitin Gwamnoni, Kungiyar Dattawan Ibo, wato Ohaneze Ndigbo da kuma Majalisar Tarayya, ta hannun Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu-maso-Gabas.

2. Dukkan Gwamnonin Kudu-maso-Gabas su tabbatar da cewa an kiyaye wadannan sharudda a Jihohin su.

3. Gwamnonin Kudu-maso-Gabas, Ohaneze Ndigbo da Mambobin Majalisun Tarayya daga wannan yankin sun yarda cewa Nijeriya daya ce, kuma ba za su bari wani ko wasu su tarwatsa ta ba.

4. Mun yarda a yi zaman sake nazarin tsara ikon Nijeriya ta yadda kowane mutum ba zai yi korafin an maida shi saniyar-ware ba.

5. Mu na kara jaddada matsayar mu cewa ba wanda ya isa ya hana a gudanar da zabe a ranar 18 Ga Nuwamba, a Jihar Anambra.

6. Mu na rokon Shugaban Kasa kuma Kwamandan Askarawan Nijeriya da ya janye sojoji daga yankin Kudu-maso-gabas, a bar ‘yan sanda su ci gaba da aikin da aka san su da shi na kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

7. Gwamnonin Kudu-maso-Gabas sun dauki kwararan matakan kare rayuka da dukiyoyin wadanda ba ‘yan asalin yankin ba.

8. Mu na tuntubar Gwamnonin Arewa, kuma sun tabbatar mana da cewa za su kare rakuya da dukiyoyin ‘yan asalin wannan yanki da ke zaune a Jihohin su.

Mun kuma amince za mu kai wa juna ziyarar karfafa dankon zumunci da yarda da juna.

9. Mun jaddada cewa za a binciki duk wasu rahotannin kashe jama’a, jikkata su ko lalata dukiyoyin su. Kuma Gwamnoni da jami’an tsaro a wancan yanki sun amince cewa duk wadanda aka kama da laifin tayar da zaune-tsayen da ya faru, tabbas sai an hukunta shi.

10. Mu na sanar da duk wani mazaunin yankin Kudu-maso-Gabas da ya ci gaba da harkokin su, ba wanda zai sake tsangwamar su. Gwamnatocin jihohin sun dauki matakan kare kowa da kowa.

11. A karshe, mu na kira ga jama’ar mu a nan Kudu-maso-Gabas su bi doka da oda.

Share.

game da Author