Jihar Gombe za ta gina sabbin manyan asibitoci 3

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Gombe Kennedy Ishaya ya ce gwamantin jihar ta kamala shirin gina sabbin asibitoci uku da kudaden da ya kai Naira biliyan 1.5 a jihar.

Ya ce za su fara gina asibitocin da zaran kudadan sun samu.

Kennedy Ishaya ya ce gwamnatin jihar za ta gina asibitocin ne a Bore Billiri, Dezam da Nyuwar sannan kowace gini za ta lashe Naira miliyan 500.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince ta yi hakan ne domin asibitin dake kauyen Bore Billiri na matukar bukatar gyara.

Bayan haka ya ce shirin ‘Sustainable Development Goals (SDGs)’ ta dauki nauyin samar wa duk asibitocin gwamantin dake jihar da kayayyakin aiki sannan ma’aikatan kiwon lafiya za ta samar da na’urar wanki na sutura a babbar asibitin gwamnatin dake jihar.

Daga karshe Kennedy ya yi kira ga ma’aikatan asibitocin dake jihar da su dage akan aikin da suke yi sannan su guji ki zuwa kauye koda sun sami canjin aiki.

Ya ce gwamanti za ta hukunta duk ma’aikacin da ya yi hakan.

Share.

game da Author