A ci gaba da ya yi wa Sanata Dino Melaye kiranye – Umarnin Kotu

0

Kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewa hukumar zabe za ta iya ci gaba da shirin yi wa Sanata Dino Melaye kiranye kamar yadda yan mazabarsa suka bukata.

Alkalin kotun Nnamdi Dimgba ya ce hujjojin da Sanata Dino ya mika gabanta bai isa ace wai sune dalilan da zai sa kotu ta dakatar da hukumar zabe daga ci gaba da gudanar da aiyukata kan haka ba.

Ya ce ba dole bane sai hukumar zabe ta sanar da Dino kamar yadda ya bukata.

Sai dai Alkalin yace hukumar zabe za ta ba Dino kofin takardun da aka mika gabanta kafin a saka sabuwar ranar fara yi masa kiranyen.

Share.

game da Author