Ambaliya: Ya kamata ayi wa Buhari Uzuri na rashin zuwan sa Benue – Gwamna Ortom

0

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya kwabi ‘yan Najeriya kan korafe korafen da suke yi cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki ziyartan mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar da aka yi a ranar 27 ga watan Agusta.

Ya ce mafi yawan mutanen da suke wannan korafin ba mazauna jihar bane sannan basu da wata masaniya akan yadda ake tafiyyar da al’amuran gwamnati.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya gaggauta daukan mataki bayan ya sami labarin halin da mutanen jihar ke ciki ta sanadiyyar ambaliyar.

‘‘Na tura shugaban hukumar NEMA da ya sanar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari halin da mutane suka shiga dalilin ambaliyar’’.

‘‘Nan da nan shugaban kasa ya aiko da ababen tallafi domin mutanen wanda shi shugaban hukumar NEMA ya kawo washe gari’’.

Samuel Ortom ya ce mutane sun manta cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ziyarce su sannan ya kuma tabbatar musu da cewa gwamantin tarayya na iya kokarinta wajen wadata wadanda abin ya shafa da tallafin da suke bukata.

Bayan haka korafe korafen da mutane ke yi akan rashin zuwan Buhari jihar Benue ta karu ne bayan da aka sami labarin cewa wai yana shirin zuwa kasar Amurka don amsa wata gayyatar shugaban kasan Donald Trump.

An karyata wannan labari ranar Alhamis bayan Buhari ya dawo daga hutun Sallan da ya yi a Daura jihar Katsina.

Maitaimaka wa shugaban kasa akan harkar yadda labarai Garba Shehu ya ce bai kamata a dinga rataya wa gwamnatin tarayya nauyin samar da tallafi ga mutanen da matsaloli irin haka ya shafa ba ganin yadda kason kudin tallafa wa mutanen irin hakan na jihohi da kananan hukumomi ya fi na gwamantin tarayya.

Share.

game da Author