An fito da sabbin hanyoyin wayar da kan yan Najeriya game bada tazarar Iyali

0

A ranar Litini ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar da fitowa da sabbin hanyoyin wayar da kan yan Najeriya game da bada tazarar iyali.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce sun yi haka ne domin kara wayar da kan mutane musamman mata kan dabarun bada tazaran iyali da inda za su iya samun su a kasar.

Ministan ya fadi haka ne a taron da masana suka yi don tattaunawa kan bada tazaran iyali karo na biyar da aka yi a dakin taro na Otel din Transcorp Hilton dake Abuja, wanda Asusun Majalisar Dinkin Duniya dake kula da yawan al’umma UNPFA da kuma wasu kungiyoyi suka halarta.

Isaac Adewole ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta amince da shirin samar da dabarun bada tazaran haihuwa don shawo kan matsalar yawan mutuwan yara da mata da kasar ke fama da shi.

A lokacin da take tofa albarkacin bakinta wakiliyar Asusun UNPFA Diene Keita ta ce UNPFA za ta ci gaba da goyan bayan Najeriya musamman a fannin bunkasa kiwon lafiyan mata da yara kanana.

Ta kara da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fama da yawan mutuwan yara da mata wanda hakan ya zama dole a nemi mafita.

Shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisan datijai Lanre Tejuoso ya jinjina wa kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ke yi wajen samar da irin wadannan dabarun don inganta iyali.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka wajen ware wa ma’aikatan isassun kudaden da za ta bukata domin samun nasara akan haka.

Share.

game da Author