Gwamnatin jihar Neja ta kara kason da take ware wa ‘yan fanshon jihar

0

Gwamnatin jihar Neja ta kara kason da take ware wa ‘yan fanshon jihar da kashi 3.5.

Kakakin gwamnan jihar Jibrin Ndace ya sanar da haka inda ya kara da cewa a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Abubakar Bello ya sa hannu a kudirin da majalisar jihar ta amince da shi na karin kason yan fanshon.

Ya bayyana cewa gwamantin jihar za ta zuba kashi 10.5 bisa 100 sannan ma’aikatan jihar za su zuba kashi 7.5 bisa 100.

Jibrin Ndace ya ce gwamnatin jihar ta yi hakan ne domin a kara kudin da ma’aikata za su samu bayan sunyi ritaya.

Ya ce ma’aikatan da aka dauka daga shekarar 1993 ne za su amfana da wannan karin.

Share.

game da Author