NNAMDI KANU: An fara zaman zullumi a Yankin Kudu-maso-Gabas, Daga Ashafa Murnai

0

A bisa dukkan alamu masu hangen nesa a yankin Kudu-maso-gabacin kasar nan sun fara ankara da sakacin da su ka yi har Nnamdi Kanu ya mike kafa a yankin ya na nema ya kira musu ruwa a lokacin da babu wurin fakewa.

Yayin da Rundunar sojojin Nijeriya ta tura dimbin zaratan sojoji a yankin nufin yin atisayi mai suna “Rawar Kumurci” wanda za su shafe kwanaki 30 su na yi. An lura cewa atisayen dai wani abu ne da Hausawa ke cewa ‘tauna tsakuwa donn aya ta ji tsoro.’

Domin ana yi wa shirin kallon wani yinkuri ne na kakkabe bore, tunziri da hauragiyar ‘yan kungiyar IPOB, masu neman a kafa kasar Biafra ko da karfin tuwo.

Tuni dai wadannan sojoji sun shiga har garin Umuahia, mahaifar Nmamdi Kanu, wanda kuma a zaman yanzu ya na gida ya lamfale, sakamakon barazanar kama shi da ya ce sojojin na shirin yi. A baya dai Kanu ya sha kumfar bakin cewa ‘kama shi ko dubu ta taru’ sai dai Nijeriya ta kone gaba daya.

A gefe daya kuma, mutanen yankin sun fara shiga taitayin su, watakila ganin yadda sojoji suka darkaki yankin makare da kayan fama.

Sannan kuma yawancin masu kaudin baki a soshiyal midiya musamman a Facebook, twitter da kuma WhatsApp, su na kumfar baki, yanzu duk jikinn su ya yi laushi, tun bayan da rahotanni su ka bulla cewa sojoji sun dangana har unguwar da Nmamdi Kanu yak e a zaune.

Na ci karo da wasu bayanai da aka fara watsawa a soshiyal midia a yau Talata, masu nuna nuna cewa bisa dukkan alamu Nnamdi Kanu ba zai samu goyon bayan da ya ke tunanin samu ba.

Sannan kuma bayanan na karin nuni da cewa da yawan mutanen yankin na gudun balbalin bala’in da ya afka musu lokacin Yakin Basasa, tsakanin 1967 zuwa 1970.

Na fassara muku wadannan bayanai har guda 15, masu yin muni da kuma kira ga al’ummar yankin cewa kada su sake su nuna wa sojoji jan-ido, burga ko wani tsageranci.

Gargadin Yin Kaffa-kaffa Da Sojoji A Yankin Kudu-maso-gabas

Ana sanar wa jama’a cewa sojojin Najeriya za su fara atisaye mai suna “Rawar Kumurci” daga 15 Ga Satumba zuwa 14 Ga Oktoba, a nan yankin Kudu-maso-gabas. Don haka ana gargadin jama’ar mu cewa su kiyaye da wannan bayanai.

1 – Ka kasance tare da katin shaidar wurin aikin ka a duk inda ka samu kan ka, don kada a tambaye ka, ka kasa bayyana ko kai wane ne.

2 – Ka da ka sake ka yi daren yawo, ko ta wane dalili.

3 – Kafin ka fita da motar ka, ka tabbatar ka na da lasisin tuki da sauran takardun shaidar mallakar motar sahihai.

4 – Kada ma ka yi amfani da mota mai duhun gilashi, ko da kuwa ka na da iznin hawan ta.

5 – Idan aka tsayar da kai a shingen jami’an tsaro, ka tabbatar ka amsa tambayoyin da aka yi maka. Kuma banda zaramboto.

6 – Kada a kuskura a tsaya yin tankiya ko gardama da sojoji.

7 – Ya fi kyau mutum ya rika zaman sa a gida, sai idan fita ta kama tilas mutum ya fita.

8 – A guji wasan kwallo a kan titi.

9 – A daina gudun motsa jiki a gefen titi.

10 – Kada ka sake ka dauki a gan ka da tutar Biafra a hannun ka.

11 – A guji kunna wakoki da karfin murya a cikin motoci.

12 – A guji tafiye-tafiye daga wannan jiha zuwa waccan. Idan tafiyar ta kama, to a fita yadda za a isa garin da za a je kafin faduwar rana.

13 – A guji dabdalar bukukuwa ko na rufe mamaci, kai ko ma wane irin buki ana tara jama’a a waje.

14 – Ya kasance mata na tafiya a kwamba, ki daina yawo ke kadai fingil-fingil.

15 – Wannan gargadi ne, a bi doka a zauna lafiya.

Daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, rahotanni sun kara bayyana cewa a ranar Talatar nan sojoji sun yi rangadi kan titunan garin Umuahia, mahaifar Nnamdi Kanu, kuma har sun dangana cikin unguwar da ya ke.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo sharuddan belin da aka gindaya wa Nnamdi Kanu har guda 12, kafin ya fita kurkukun Kuje, Abuja. Daga cikin wadannan sharudda 12, Kanu ya karya guda 8, wadanda dalili kenan ma gwamnatin tarayya ta nemi kotu ta bai wa jami’an tsaro iznin kamo shi a sake kullewa, tunda ya sake karya doka.

Share.

game da Author