Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya caccaki manyan ‘yan siyasa, alkalai da lauyoyin kasar nan dangane da yadda ake zubar wa shari’a mutunci a cikin kotu.
Onnoghen ya yi wannan caccaka ne a wurin Taron Lauyoyi na Kasa da a kan gudanar a duk shekara, a jiya Litinin, a Kotun Koli, Abuja.
Ga kadan daga cikin jawabin nasa mai zafi PREMIUM TIMES HAUSA ta tsakuro:
1. Abin haushi ne da cin mutuncin kotu ka ga ‘yan siyasa na zuwa kotu da lauyoyi masu kare su har sama da 100.
2. Su na zubar wa kotu da shari’a mutunci idan su ka cunkushe a cikin dakin shari’a.
3. Babu abin kunya da ya wuce ka ga wai a cikin kotu har a kasa kan tayil lauyoyi ke zama idan ba su samu wuri ba.
4. Daga yau din nan ina so alkalai su sani, kada a kara barin wani dan siyasa ya shiga kotu da lauyoyi sama da 5.
5. Ba za mu kara lamuntar alkalai da lauyoyi na hada baki su na yi wa shari’u walagigi ba.
6. Za a rika kamawa tare da hukunta duk alkalin da aka samu ya na yi wa shari’a dungu, walagigi ko tafiyar-maciji.
7. Za a rika kamawa kuma ana hukunta lauyoyin da ke wa shari’a ‘yar-burum-burum tare da rainawa wa kotu wayau.
8. Daga yanzu za a fara ganin canji, domin jiya ba yau ba ce.
KWARYA-KWARYAR NASARA A 2017:
Walter Onnoghen ya bayyana cewa a cikin zangon shekara daya na 2016/2017, Kotun Kolin kasar nan ta samu nasarar yanke hukunce-hukunce masu yawa, idan aka kwatanta da shari’un shekarun baya:
An yanke hukuncin shari’u har 243 daga cikin 1,362 na kararrakin da aka kai a Kotun Koli.
Ya ce daga cikin kararrakin da aka kai a Kotun Kolin, 83 wadanda ke da alaka da siyasa ne, 675 na mu’amaloli ne tsakanin jama’, sai kuma 208 na laifuka ne.
Alkalin Alkalan ya kara da cewa akwai daga ciki kuma har 394 wadanda daukaka kara ce. Daga cikin su kuwa 96 duk na rigimar siyasa ce, 174 na mu’amalolin jama’a ne, sai 128 na aikata laifuka ne.
Ya ce gaba daya idan aka hada, sun tashi 1362 kenan. Daga cikin su ne Onnoghen ya ce an yanke hukunci 243.
Ya kuma yi bayanin cewa gargadin da ya yi zai sa a rika samun yanke hukunci a cikin hanzari a kotuna.