Tunda El-Rufai ya ga Buhari ya dawo, ba zai samu mataimakin Shugaban kasa ba ya fara yi masa dan koro – Shehu Sani

1

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya ce tsayar da gwamnan jihar Nasir El-Rufai da jam’iyyar a jihar ta yi labarin gizo da Koki ne kawai amma bashi da wani tasiri.

Shehu Sani ya ce gwamna El-Rufai ya tara abokansa da ‘yan koran sa ne kawai suka wani ce sun tsayar dashi wanda zai rike wa jam’iyyar kambu a zaben gwamna a 2019.

Ya ce El-Rufai yana kokarin makalewa ne da farinjinin Buhari domin samun jama’a.

” Tsayar da El-Rufai dan takaran gwamna a 2019 kamar tsayar da gurbataccen shara ne da ba shi da amfani.”

” Jingina kansa da yake yi da Buhari na neman suna ne kawai da jama’ da kuma samun madafa a siyasa.”

” Tun da El-Rufai ya ga cewa Allah ya ba Buhari lafiya ya dawo kasa sumul, ya tsiri wata sabuwar hanyar nuna wa Buhari soyayya tunda ya ga ba burinsa na zama mataimakin shugaban kasa ba zai tabbata ba kuma.”

” Soyayyar da El-Rufai ya ke nuna wa Buhari, ta Karya ce ba ta saboda Allah bace. Yana yi ne don siyasar sa kawai. Lallai Buhari yayi hattara da yadda El-Rufai yake tsuguna masa har guiwa.”

” Mutumin da ya ke gadara da shine yayi sanadiyyar mutuwar tsohon shugaban kasa Yar’Adua zai iya yin Komai.

Share.

game da Author