Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa yawancin garkuwa da mutane da ake yawan yi, duk ‘yan sanda ne ke aikatawa.
Gwamnan ya kuma zargi jami’an ‘yan sanda da shigewa gaba wajen aikata miyagun laifuka daban-daban. Ko da ya ke dai rundunar ‘yan sandan ta yi gaggawar maida wa gwamnan martanin cewa maganar ta sa shirme ce, kuma yaudarar jama’a ce kawai.
“Duk abin da gwamna Wike ya fada, ba abin mamaki ba ne, domin kowa ya san mugun nufin gwamna Wike.
“Ku kan ku ma kamata ya yi ku yi biris da surutan sa. ‘Yan sanda ba su shigewa gaba wajen aikata mugayen laifuka. Mu fa jami’ai ne masu fada da kuma kama masu aikata mugayen laifuka.”
Haka kakakin rundunar ‘yan sandan kasar nan, Jimoh Moshood ya bayyana wa PREMIUM TIMES a ranar Talata.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin APC na daure wa wasu jami’an ‘yan sanda gindi domin su biya mata bukata a lokacin zaben 2019. Duk kuwa da cewa an same su dumu-dumu da hannu cikin aikata wasu alifuka.
Wike ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar lauyoyi na Afrika, a gidan gwamnatin Fatakwal da daren Litinin.