Akalla ‘yan Najeriya 540 aka yi shirin korowa daga Libya tun daga ranar 10 Ga Agusta, 2017. Darakta Janar ta Hukumar Hana Safarar Mutane, NAPTIP, Julie Okah-Donli ce ta bayyana haka.
Ta ce za a rika maido da su ne kashi-kashi, ta hanyar maido da 180 a kowane zango, har a kwaso su baki daya.
Okah ta bayyana haka a garin Osogbo, yayin da ta ke jawabi wajen bude ofishin hukumar a shiyyar Osogbo.
Daraktar ta kuma kara da cewa daga watan Fabrairu zuwa yau, sama da ‘yan Nijeriya 2000 aka dawo da su gida daga kasashe daban-daban cikin duniya.
Ta kuma yi albishir da cewa hukumar NAPTIP ta ceto kuma ta tallafa wa sama da mutane dubu 12,000 wadanda aka yi safarar su daga shekarar 2003 da aka kafa hukumar zuwa yau.
Ta ce an kuma gurfanar da masu laifin safarar mutane har 325 a cikin wadannan shekaru da su ka gabata zuwa yau.
Sai dai kuma ta nuna matukar damuwar ta dangane da yawan koro ‘yan Najeriya da ake yi daga kasashe daban-daban, musamman ma daga kasashen Afrika, abin da ta ce ya na da firgitarwa ainun.