Jihar Kebbi za ta gyara dokar karba da tara haraji a jihar

0

Kwamishinan kudi na jihar Kebbi Ibrahim Augie ya ce gwamantin jihar za ta gyara dokar karban haraji domin bunkasa karbar haraji a jihar.

Ya fadi haka ne da yake bayanin kan kudaden da jihar ta tara wajen karbar haraji a cikin shekaru biyu da suka gabata da ya kai naira biliyan 6.4.

Ibrahim Augie ya ce wannan kudin harajin da suka tara ya yi kadan idan aka kwatanta shi da yawan kudin da za a samu daga hannayen wanda basa biyan haraji a jihar.

Ya ce saboda hakan ne gwamantin ta amince ta gyara dokar biyan haraji a jihar ta hanyar bankado mutane da kamfanoni da basa biyan haraji a jihar domin su fara biya.

Ya kuma kara ta cewa dokar da za a gyara zai taimaka wajen dakile duk hanyoyin wawushe kudin harajin da wasu ma’aikatan ke yi.

Share.

game da Author