Wani sabon binciken da PREMIUM TIMES ta yi, ya tabbatar da cewa kamun da aka yi wa Sajen Musa, wanda shi ne babban dillalin sata da sayar da kayan gidan Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, a Gwarimpa, Abuja, ba shi ne na farko ba.
Kwakkwarar majiya ta tabbatar da cewa an fara kama shi ne a wata rana da wani makwabcin gidan ya je cigiyar wata rumfa ta sa, amma sai ya same ta a hannun Musa, a gidan Jonathan.
Majiyar PREMIUM TIMES ta ce wata kwantina ce aka shiga gidan makwabcin aka fasa, aka sace rumfar, wadda aka fi sani da canopy.
“Da aka kama Musa aka kai shi ofishin ‘yan sanda da ke Gwarimpa, sai wani insifeto da su ke aiki a gida daya da shi ya je ya yi belin sa, a bisa sharadin zai sake gabatar da shi a ranar Litinin.”
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an je har gidan Jonathan an cafke Insifeto bayan da ya kasa kai Sajan Musa ofishin ‘yan sanda a ranar. Sufeton nan ya shaida wa jami’an ‘yan sandan binciken kwakwaf cewa lallai Musa ya gudu, amma ya na da gida a Dikwa, wani garin ka-zo-na-zo da ke Arewacin Dei-dei.
PREMIUM TIMES ta ji cewa ashe Musa ya sayi gida ne a Dikwa, kusa da Dei-dei. Amma bayan guduwa da ya yi, sai ya garzaya ya sayar da shi arha bagas. Sai dai bai taki sa’a ba, domin rabin kudin kawai aka ba shi, rabin kuma aka ce sai ranar Litinin.
Yayin da ‘yan sanda su ka tasa keyar wannan Insifeto zuwa gidan Musa a Dikwa sai su ka taras da wanda ya sayi gidan, kuma ya yi musu bayanin cewa Musa ya na wani Otal kwance, ya na jiran ya kira shi ya karbi cikon kudi.
Nan ne fa ‘yan sanda su ka ce to ya kira Musa ya ce masa ya zo ga cikon kudin sa sun hadu. Ko da Musa ya ce ga shi nan zuwa, sai ‘yan sanda su ka yi kwanton-bauna, inda ya na zuwa gidan sai suka yi cacukui da shi, nan take suka buga masa ankwa a hannayen sa.
Wani ganau ba jiyau ba, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa:
“Da ido na na ga Musa da ankwa wadda aka daure hannayen sa ta bayan sa aka daure. Na fito daga ofishin kenan, sai na ga ana sauko da shi daga cikin wata mota. Ya na sauka kasa, sai na ga ankwa a hannayen sa. A zuciya ta na ce to yau ba rana ta baci, an kamo mai kamowa.”
Tun a ranar Alhamis dai rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta bada sanarwar korar Musa da wasu ‘yan sanda hudu daga aiki, a bisa laifin kantara mummunar sata a gidan Jonathan.
Rundunar ta kuma bada sunayen wasu sufeton ‘yan sandan da ta ce su ma su na da hannu, ga Mataimakin Sufeton ‘Yan sandan Shiyyar Abuja, domin a hukunta su.
PREMIUM TIMES ta gano cewa cikin su har da Insifeton da ya karbo belin Musa a kamun farko da aka yi masa. Dukkan su biyu din dai a gidan Jonathan su ke gadi.