Saurari abin da Uba Sani ya ce kan harin da aka kai NUJ

0

Bayan rahotanin da ake ta yadawa game maganganun da mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkar siyasa Uba Sani wai ya yi, gidan jaridar Premium Times ta samu gaskiyar abinda da ya fadi sabanin abinda ake ta yadawa wai ya fadi game da harin da aka kai wa wasu Sanatocin jihar a Kaduna.

Da aka tambayi Uba Sani game da wannan hari, ya ce gwamnatin jihar ta kafa wata kwamiti domin gudanar da bincike akan hakan.

Ya ce bayanan bincike da ake gudanar wa da ya fara fitowa sun nuna cewa wasu matasa ne suka harzika bayan rashin cika alkawura da wasu daga cikin sanatocin suka yi wa matasan.

Uba Sani ya ce sun gano cewa wasu daga cikin yan siyasar basu cika wadannan alkawura ba saboda haka ne matasan suka far musu.

Uba Sani ya ce ana nan an ci gaba da bincike akan haka.

Share.

game da Author