Hukumar Zabe ta gargadi jam’iyyu su daina giribtun yawan kai kararraki

0

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta roki jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa su fito da hanyoyin samun daidaito a tsakanin su, maimakon su rika garzayawa su na cika kotuna da kararraki na giribtu.

Wannan sharawa dai Hukumar Zaben ce ta bayar da ita a yayin wani taro a Abuja, inda kuma ta Nina damuwa da irin yawan yadda ‘yan siyasa ke kin bin umarnin ko hukuncin da wasu kotuna su ka gabatar.

Ta kuma yi nuni da cewa abin mamaki ne inda ‘yan siyasa ke daukar wasu kararraki da Babbar Kotun Daukaka Kara ko Kotun Koli su ka zartas da hukunci zuwa wasu kananan kotuna.

Ya ce irin wannan giribtu da ‘yan siyasa ke yi ya na kawo tsaiko da tarnaki wajen kokarin Hukumar Zabe na tabbatar da tafarkin dimokradiyya mai dorewa a kasar nan.

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mahmood Yakubu, ya kara jaddadawa a wurin taron ya kuma nuna damuwa cewa hakan da ‘yan siyasa ke yi ya na dagula manhaja da jadawakin ranaku da lokuttan gudanar da zabe.

Yakubu ya buga babban misali da harigidon rigimar siyasar jihar Anambara, inda har yau ba a gudanar da zabe ba a yankin Anabara ta Tsakiya, saboda jam’iyyu sun koma sun kalubalanci hukuncin da manyan kotuna su ka aiwatar.

Share.

game da Author