Rundunan ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani limamin coci da laifin aikata lalata ga wasu tagwaje mata da Gambonsu yan shekara 13 da 11.
Kakakin ‘yan sandar jihar Magaji Majiya ya sanar wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa sun kama Samuel John ne bayan karan da iyayen da makwabtan yaran su ka kai ofishinsu.
Magaji Majiya ya koka akan yadda fyade ke neman ya zama ruwan dare a jihar duk da kokarin da rundunar ‘yan sanda, kungiyoyi masu zaman kansu a jihar ke yi don kawar da wannan matsala da ake fama dashi.
Ya ce a cikin wannan wata na Agusta rundunar ta saurari kararraki na fyade da ya kai 34. Misali wani magidanci Nuruddeen Abubakar dan shekara 40 da ke zama a kwatas din Unguwa Uku ya dinga yi wa yar cikinsa yar shekaru 14 fyade wanda tayi ta zubar da ciki har sau uku.”
“Haka nan muka kama wani Musbahu Ibrahim dan shekara 25 mazaunin kwatas din Zangon Marikita da laifin aikata lalata da ‘yar goggonsa’.
“Mun kuma kama Dahiru Haruna da Hamza Lawan mazauna kwatas din Sheka da laifin aikata lalata da wani yaro dan shekara tara’.
Discussion about this post