Duk wanda aka kama na yada jita-jita ko hotunan da zai iya tada zaune tsaye zai yaba wa aya zaki – El-Rufai

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga mutanen jihar da su guji yada jita-jitan da ka iya tada rikici a jihar musamman a karamar hukumar Kajuru da sauran sassan jihar.

Da take sanar da haka a zaman kwamitin tsaro da akayi a Kaduna, kwamitin tayi kira ga mutane da su daina yin amfami da kafafen yada labarai musamman shafuna Facebook da sauransu wajen saka hotunan da zai iya tada zaune tsaye a jihar.

Da yake sanar da wannan matsayi na gwamnati bayan kammala taron, kakakin gwaman jihar Samuel Aruwan a wata takarda da ya sa wa, EL-Rufai yace duk wanda aka kama yana aikata hakan zai yaba wa aya zaki.

Akalla mutanen 33 suka rasa rayukansu a rikicin Kajuru wanda mafi yawansu Fulani ne.

Gwamnati ta yanke wadannan hukunci:

1. An kama wasu daga cikin wadanda suke da hannu a rikicin in da yanzu haka ana gudanar na bincike akansu sannan wasu na fuskantar shari’a a kotunan jihar.

2. Jami’an tsaro a jihar na gab da kamo wadanda ake zargin su ke rura wutan tada zaune tsaye a jihar.

3. Gwamnatin jihar a karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai ba za ta yi kaskasa ba wajen hukunta duk wanda yake neman ya da da zaune tsaye a jihar sannan zata samar wa mutanen jihar didaituwa musamman wadanda ya shafi ‘yan cinsu da kwatanta adalci da tsaro a tsakanin mutanen baki jihar.

4. Gwamnatin jihar na amfani da dabaru daban-daban don ganin an sami tabbatacciyar zaman lafiya sannan gwamnan ya yi kira ga kauyukan da rikicin ya shafa da su guji duk abin da zai ingiza su ga daukan fansa ta kowace hanya.

5. Gwamnatin jihar ta kara jaddadawa mutanen jihar cewa lallai za ta hukunta duk wanda ta samu yana da hannu a rikicin da ya faru a karamar hukumar Kajuru.

Share.

game da Author