AMBALIYA: Gwamnatin Jihar Yobe ta kai wa mutanen Jajikaji dauki

0

A ranar Asabar ne mazaunan kananan hukumomin Jajikaji da Karasuwa dake jihar Yobe suka rasa matsugunin su sanadiyyar ambaliyar ruwan saman da akayi kamar da bakin kwarya a yankunan.

Shugaban karamar hukumar Jajikaji, Ubaliyo Gambo ya sanar da hakan wa manema labarai ranar Lahadi sannan ya kara da cewa sama da mutane 100 ne suka rasa gidajensu da gonakinsu sanadiyar ruwan.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Yobe SEMA Musa Jidawa a lokacin da suka zo ziyarar yin jaje ga mutanen yankin ya ce sun zo ne domin su samar wa mutanen da suka yi hasarar dukiyoyinsu agajin gaggawa da yi musu Allah ya kyauta.

Bisa ga abin da ya gani Musa Jidawa ya ce za su taimaka wa mutanen ta hanyar samar musu da wani wurin zaman sannan a gina musu magudanar ruwa.

Ya ce ya yi murna matuka da hadin kan da suka samu daga mazauna garuruwan.

Share.

game da Author