Buhari ya koma bakin aiki

1

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aika da wasika a Majalisar Tarayya, inda ya ke bayyana musu dawowar sa bayan hutun kwanaki 103 da ya yi a London, ya na kuma mai sanar da su cewa zai koma bakin aikin sa.

A cikin wasikar da ya sa wa hannu da kan sa, kuma aka aika wa Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kuma Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara, sa’o’i kadan bayan gabatar da jawabin sa ga al’ummar Najeriya a yau Litinin.

Haka dai kakakin yada labaran sa, Femi Adesina ya bayyana.

“Kamar yadda dokar kasa ta umarce shi, Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ya aika a majalisar tarayya, ya na mai sanar da su cewa ya koma bakin aikin sa, bayan hutun da ya dauka zuwa London.” Inji Adesina.

Share.

game da Author