KIRA GA FAYOSE: Ka fito ka kashe kanka tunda Buhari ya dawo kamar yadda kayi Alkawari

0

Daruruwan magoya bayan kungiyar APC na jihar Etiki da wasu kungiyoyin sa kai, sun gudanar da jerin-gwanon nuna murnar dawowar Shugaba Muhammadu Buhari, bayan shafe kwanaki 103 da ya yi zaman jiyya a London.

Gamayyar masu jerin gwanon sun rika yin habaice-habaice ga gwamnan jihar, Ayodele Fayose, wanda su ka ce tun bayan tafiyar Buhari ya ke ta kitsa labarai na karya da izgilanci ga shugaban kasa, inda ya ke cewa “Buhari na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai tun a ranar 6 Ga Yuni.” har ya yi rantsuwar cewa matsawar ya dawo Najeriya da kafafun sa, to zai kashe kan sa.

Masu jerin gwanon dai sun haddasa cinkoson ababen hawa yayin da su ke tafiya suna rera wakokin habaici ga Fayose da kuma jam’iyyar PDP.

Da ta ke jawabi, shugabar riko ta Jam’iyyar APC a jihar Ekiti, Kemi Olaleye ta kalubalanci Fayose da ya fito ya cika alkawarin kashe kan sa da ya yi, tunda Buhari dai ya dawo.

Ta ce Fatose ya na nuna gabar sa ta na wuce wuri, maimakon ya tsaya kan adawa mai ma’ana kawai. Ta kara da cewa “duk mutumin kirki ba zai goyi bayan irin yadda Gwamna Fayose ke zubar musu da mutunci wajen kin ganin girman na gaba da shi.”

“Ku dubi Gwamna Wike na Ribas mana, duk da irin adawar da ya ke yi, sai da garzaya Abuja aka tarbi Shugaban Kasa tare da shi. Amma mu ba mu san irin wannan dabi’a ta Fayose ba. Ni dai na san al’adar mu ba ta koya mana irin wannan zubar da mutunci ba.”

Share.

game da Author