A guji zuwa rafi: Kira ga mutanen kauyukan Jigawa

0

Rundunan ‘yan sandan jihar Jigawa ta koka kan yadda ruwa a rafunan jihar ke yawan cinye mutanen.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Abdul Jinjiri ne ya sanar da hakan wa manema labarai a Dutse ranar Talata.

Abdul Jinjiri ya ce kogin Ringim, Guri, Kiyawa da Dutse ta cinye mutane manya da yara kanana 11 cikin wata daya.

Jinjiri ya yayi kira ga mutanen garuruwan musamman wadanda basu iya ruwa ba da su guji zuwa rafi sannan su rage yin su.

Daga karshe yayi kira ga iyaye su sa ido kan ya’yansu.

Share.

game da Author