Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce ana samun kudin shiga da ya kai naira miliyan daya duk rana ta hanyar jigilar matafiya daga Kaduna zuwa Abuja ta jirgin kasa.
Ya ce hakan ya samu ne dalilin cunkoson matafiya da ake samu a tasahr jirgin wanda sukan yi haka ne don gujewa kicibir da masu garkuwa da ake yawan samu a titin Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce yanzu haka ribar da suke samu ya fi kudaden da suke kashewa wajen gyara taragon jiragen.
Amaechi ya ce gwamnati na kokarin rageyawan tallar da wasu ke yi a tashar musamman tashar Idu da ke Abuja sannan za ta karo wasu jiragen kasan guda 10 nan da watan Oktoba.