Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya yi tir da yadda wasu suka fitar da wani bidiyo nasa tare da wasu ‘yan mata ya na saka kaya a wani daki.
Sanata Bukar ya ce wannan abu ya bakanta masa rai domin yasan wasu ne suka yi haka don su bata masa suna.
“ Wannan abu ne da ya shafi balagaggu biyu. Menene ya hada kusantata da wata mace abin tattaunawa ga kowa da kowa.
Da zaran mutum ya nemi wani abu a wurinka kuma bai samu ba sai ka ga ya nemi wani hanya da zai tozarta ka.”
A bidiyon an ga Sanata Bukar yana saka wandonsa bayan ya fito daga dakin wanka, ga wasu kuma ‘yan mata biyu suna tare da shi a tsatstsaye.
Sanata Bukar ya ce babu wani wanda zai yi wa bayani kan yaduwar wannan bidiyo domin abu ne da yake na sirri aka fidda shi don tazartashi.
“ Da ace na aikata fyade ne da labarin ya canza salo, ko kuma ya zama wani abin da bam. Amma shikenan kuma ace wai mutum bashi da wata dan lokaci da zai yi rayuwarsa ba tare da an bishi da kulle-kulle ba saboda kawai ina dan siyasa.”
Ya ce lallai ya tuna lokacin da yake tare da wadannan mata, daya daga cikinsu na daukar bidiyo amma da yake ba wani abu bane yake faruwa duk da ya tambayi dalilin haka suka ce babu komai abin bai tada masa da hankali ba a wancan lokacin.
Sanata Bukar ya kara da cewa lallai zai sa a binciki wannan rashin hankali da akayi masa.
Discussion about this post