Yan Boko Haram 700 sun mika wuya

0

Babban Hafsan Sojojin kasan Najeriya Janar Tukur Burutai ya ce sama da yan Boko Haram 700 ne suka mika wuya ga sojin Najeriya.

Tukur Buratai ya sanar da hakan ne ranar Litini a taron baje kolin hotunan da aka yi na tunawa da aiyukkan dakarun sojin Najeriya.

‘’Za mu sami sauran bayanai daga wajen jagoran sojojin da suke aiki a Maduguri. Sannan kuma ina yi wa dakarun sojojin kasa, sojin ruwa da na sama da suke aiki a yankin arewa maso gabacin kasar nan godiya kan nasarorin da muke ta samu’’.

Bayan haka kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya ce cikin wadanda suka mika wuyan 70 daga cikinsu an gama tantance su kuma ana inda wasunsu sun yi daidai da wadanda ake nemansu dama ruwa a jallo.

Share.

game da Author