A cikin makon da ya gabata na ci karo da wani bayani mai ban-haushi, duk kuwa da cewa na dade da sanin bayanin. A zato na zuwa wannan shekarar abin ya canja, an samu cigaba fiye da shekarun baya. Amma kasancewa Hukumar Kula da Ilmin Firamare ta Kasa, wato UBEC ce da kan ta ta bayyana a makon da ya gabata cewa kashi 71 bisa 100 na yaran da ke gararamba a kan titi ba su zuwa makaranta, duk a Arewa suke, abin ya tayar min da hankali sosai.
Ganin haka, sai na shiga tunani da bincike domin ko zan iya samun akasin haka. Ina da makwauci da ke koyarwa a makarantar firamare ta gwamnati. Ranar Juma’ar da ta gabata, sai na tunkare shi da waccan kididdiga da UBEC ta yi mai nuna yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Arewa.
Maimakon malamin nan ya yi mamaki ko bata rai, sai ya yi dariya sannan ya ce min, “yallabai wannan ai ba tashin hankali ba ne. Tashin hankali ai sai ka shiga makarantun firamare na gwamnati. Wadanda ake cewa su na karatun su ne ma masu matsala, ba wadanda ba zu zuwa makarantar ba.’
Ya ci gaba da ba ni labarin matsaloli da kuma yadda ilmin firamare a makarantaun gwamnati suka lalace kwata-kwata, duk kuwa da bilyoyin kudaden da gwamantin tarayya da na jihohi ke ware wa ilmin. Tambaya a nan, shin ana kashe kudaden a fnnin ilmin kuwa, ko dai kashe-mu-raba ake yi da su?
“Ka ga dai farkon fara koyarwa ta a wannan makaranta da na ke koyarwa a cikin wannan shekara, dukkan ‘yan aji hudu sai da na koya musu yadda za su rubuta sunan su da sunan iyayen su. Sannan daga aji daya har zuwa aji shiga za ka samu yaro sama da 100. To don Allah ya za a yi ka koya musu har su gane? Abin takaici kuma a kasa sun ke zaune.” Haka malamin ya shaida min.
Kamar yadda ‘yan firamare ta gwamnati suke a Kano, haka suke a Katsina, haka a Sokoto haka a Kebbi, ballantana Yobe ko Bauchi. A da rajistar da ke dauke da sunayen daliban kowane aji, ba su wuce 40. Amma a yanzu rajistar dalibai a jihar Kano ta na dauke da sunayen dalibai 160, wato shafi daya dauke da sunayen maza 80 ko sama da haka, wani shafi kuma dauke da sunayen mata 80 ko kasa da haka, kuma duk a aji daya.
Malamin nan ya ce min a yanzu fa saboda yawan yara a aji, ba a ma cika yin kiran sunaye da safe ba. Kenan malami bai ma san wanda bai zo ba ko kuma wanda bai zuwa dungurugum. Idann mutum ya na ji ko ganin irin wannan abin takaici, sai ya yi tunanin shin ina ministan ilmi kuwa? Ya na sane da wannan babbar matsala? Daga lokacin da ya hau mukamin minista, ko ya taba shiga wani ajin firamare ta gwamanti a Karamar Hukumar Kura ta jihar Kano kai ko ma Karamar Hukumar da aka haife shi a jihar Bauchi?
Shin kwamishinoni kan kai ziyara makarantun nan ko kuwa sai dai kasafta kudin ilmi kowane wata? A lokacin da na yi karatun firamare, komai kyauta ake bayarwa a makaranta. Biro ko fensari kawai yaro zai rika saye. Amma hatta littattafan karatu da na rubutu duk kyauta ake bayarwa a makaranta. Amma yanzu komai sai iyayen yaro sun sai masa, kuma a makarantar gwamnati wadda a wancan lokacin kudin da jihohi ke samu ba su ma kai farashin bajimin sa guda daya tal a yanzu ba. Amma duk da haka ilmin a kyauta aka rika ba mu shi. A yanzu kuwa da ana koyon abin kirki ma, to da dan dama-dama. Amma duk inda ka ji wani dalibi ya yi bajinta, ba za ka taba jin ya fito daga makarantar gwamnati ba, sai dai makarantu masu zaman kan su.
Kiri-kiri wasu gwamnoni a nan Arewa suka yi alkawari idan sun ci zabe, to za su cire ‘ya’yan su daga makarantu na kudi su maida su makarantun gwamnati su na karatu tare da ‘ya’yan talakawa. Duk sun ci zaben amma shiru ka ke ji, kuma an sa musu ido.
Idan mai karatu zai tsaya ya yi nazari, zai fahimci kawai dai dan talaka ne aka bari a makarantun firamare na gwamnati. Makarantun sun kusa komawa zaurukan hira da cibiyoyin tatsuniya da wasannin harbat-ta-Mati kawai. Daga inda aka ce ‘yan aji hudu ba mai iya rubuta sunan sa da na mahaifin sa, to me ya rage kuma? Sai mu tambayi kwamishinoni, shin boko yara ke zuwa koyo ko dai bokoko?
Kun ga kenan ashe gwamnati ce ke kyankyashe yaran da ba su zuwa makaranta da kan ta. Shi ya sa za ku ga iyayen yara a kauye su na hana ‘ya’yan su zuwa sakandare ko da kuwa gwamnari ta dauke su ba tare da sun ci jarabawa ba. To me dan ka zai je ya koya a sakandare har tsawon shekara shida, bayan ya shafe shekara shida a firamare bai iya rubuta sunan sa da na ka sunan ba?
Yawanci dalili kenan a birane talakawa ke dara wa ‘ya’yan su talla su na bin lunguna da kasuwanni su na tallar awara ko nakiya da alkaki, saboda sun kammala firamare ba su iya rubuta sunan su ballantana sunan iyayen su. Shi kuma minista ba abin da ya shafe shi, domin babu ‘ya’yan sa a makarantun firamare Ina ruwan kwamishina ko gwamna, kai dai ka bar su wajen bada labarin kwangilolin gina ajujuwa ko yi wa ajujuwa kwaskwarima. Da an buda baki sai a ce an kashe bilyan kaza. Amma idan aka ce wa dan firamare “how old are you?” sai ya ji kamar Zabarmanci ka ke yi masa, ba Turanci ba.
Da yawan malaman firamare a yanzu ba su wuce su zauna ajin firamare a koyar da su ba. wanda ya yi gardama to ya jaraba shida daga cikin goma ya sha mamaki. Kowa babu abin da ke zuciyar sa sai iya lissafin saura kwana takwas wata ya kare a yi albashi kawai.
Da yawan malaman firamare a yanzu acaba su ke yi ko tuka baburan A Daidaita Sahu. Wasu ma jogon kaji su key i su na bin kasuwannun kauyuka a ranakun karatu. To kai ya ka gani? Tunda minista da kwamishina bai damu da lalacewa karatun firamare ba, malami na ganin ai shi ma ba sai ya takarkare ya tilasta wa yaro sai ya iya rubuta sunan sa ba. Tunda za a bayar da kwangiloli malamai su karbi albashi, wa zai koma ta kan karatun ‘yan firamare, ‘ya’yan talakawa masu karatun bokoko?