Hukumar Zabe Ta Kasa ba ta yi watsi da kiranyen Dino Melaye ba

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta Kasa ta bayyana cewa karya da sharri ne kawai ake yi wa hukumar da kuma shugaban ta, Mahmood Yakubu cewa ta dakatar da batun kiranyen Sanata Dino Melaye ne domin barazanar da majalisar dattawan ta yi cewa za ta binciki ayyukan da aka gudanar a Hukumar Tallafin Manyan Makarantu, wato TETFUND, wadda shugaban na INEC ya shugabance ta a baya.

A cikin wata takarda da babban kwamishina a hukumar, Ikechukwu Ibeanu ya sa wa hannu, ta bayyana cewa: ‘’Hukumar na shaida wa duniya karara cewa wadannan rahotanni ba gaskiya ba ne, sharri ne kawai na mahassada. Lamari ne da ya ke a bayyane cewa, a ranar 21 ga watan Yuni da ya gabata, wasu jama’a masu rijistar kada kuri’a daga mazabar dattawa ta Kogi ta Yamma, sun gabatar wa hukumar takardar korafinsu tare da bukatar a yi wa sanata mai wakiltar shiyyarsu kiranye.”

Ibeanu, wanda shi ke rike da shugabancin hukumar na riko, kasancewa Mahmood ya tafi taro kasar Corte D’voire, ya kara bayar da hasken cewa: “Daga nan hukumar ta tabbatar da karbar wannan takardar korafin, sannan ta sanar da sanatan da lamarin ya shafa a rubuce. Bayan haka ne, kuma bisa la’akari da hurumin da hukumar ke da shi kamar yadda yake kunshe cikin kundin tsarin mulki a sashe na 69 da na 110 cikin kundin tsarin mulki na 1999 na tarayyar Najeriya, da kuma sashe na 116 na dokokin zabe na shekarar 2010, hakan ya sanya a ranar 3 ga watan Yulin 2017, hukumar ta sanar da jadawalin tsare-tsare da kuma lokutan da ayyukan yi wa sanatan kiranye za su gudana.’’

‘’Abu na farko da hukumar ta shirya aiwatarwa a tsare-tsaren nata, aiki ne da ya kamata a ce ya gudana a ranar 10 ga watan Yulin da ya gabata, ta hanyar bayyana sharudda ko matakan kiranyen inda za ta manna wata sanarwar tantance jama’a a mazabar Kogi ta Yamma a ofishin hukumar da ke Lokoja. Sai dai, a daidai wannan rana ne hukumar ta samu sakon umarni mai dauke da kwanan wata, 6 ga watan Yulin 2017 daga Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda aka bukaci dukkanin bangarorin su dakatar da komai har sai bayan kammala sauraren karar da sanatan da lamarin ya shafa ya shigar a kotu in da ya bukaci kotu ta dakatar da hukumar daga yin aiki a kan korafin da jama’ar mazabar Kogi ta Yamma suka gabatar mata.

Shugaban na riko wanda kuma ke rike da mukamin kwamishina na kasa a hukumar zaben, ya kara yin bayanin cewa: “A daya bangaren, bayan amincewa da bukatar da Sanata Milaye ya nema ga kotu, alkalin kotun ya sanya ranar 29 ga watan Satumba, 2017, a matsayin ranar da za a saurari karar. Duba da wannan rana da kotun ta tsayar kuwa, zai kasance kenan kwanaki 90 da ya kamata hukumar ta INEC ta kammala aikin kiranyen a tsakaninsu kamar yadda dokar kasa ta tanadar sun kare.

Wannan mataki ya jefa hukumar cikin damuwa matuka saboda haifar mata da tsaiko da aka yi a kan batun da dokar kasa ta ba ta ikon tabuka wani abu a inda ya dace. Bayan taron mako-mako da hukumar ta saba gudanarwa, ya sanya a ranar 13 ga watan Yuli, 2017, hukumar ta ga dacewar ta yi biyayya ga umarnin da kotu ta bayar.”

Don haka, batun cewa matakin yi wa kotu biyayya da hukumar ta dauka na da alaka da kudirin binciken asusun tallafa wa manyan makarantu, wato TETFUND a takaice, da Majalisar Dattawa ke da shi karya ne, kuma wani shiri ne na neman bata wa hukumar suna. Wani abin da ya kamata a sani shi ne, shi kansa shugaban hukumar INEC bai halarci taron da aka dauki matakin yi wa umarnin kotu biyayya ba. Hasali ma, yanzu haka shugaban hukumar ya jagoranci wata tawaga zuwa wajen wani taron kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) domin tattauna batutuwan da suka shafi harkokin zabe.

Da wannan, matakin yin biyayya ga umarnin kotu da hukumar ta dauka, ta yi hakan ne domin jan hankalin Alkalin Alkalai na kasa game da wasu abubuwa da suka shafi Babbar Kotun Tarayya. Kuma ko kadan, hakan ba shi da wata alaka da take-taken neman dakatar da shirin yi wa Sanata Milaye kiranye, wanda tuni shirin kiranyen ya kankama.

A karshe, hukumar ta sanar da al’umar Nijeriya cewa, za ta ci gaba da aiwatar da harkokinta kamar yadda dokar kasa ta halasta mata ba tare da wani tsoro ko shakka ba, nuna rangwame ko tausayi ga kowa ba.

Share.

game da Author