Rundunar Soji ta gano sabuwar maboyar Boko Haram

0

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta gano wata sabuwar maboyar Boko Haram, kuma tana shirin kai ma wannan wuri hari domin tarwatsa su.

Wannan wuri na kan tsibirin Tafkin Chadi ne.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Kwamandan riko na bataliyar GOC 8, wadda, Stevenson Olabanji, a lokacin da ya ziyarci dakarun bataliya ta 118 a sansanin yankin Gudumbali, cikin karamar hukumar Guzamala, jihar Barno.

Kakakin rundunar Timothy Artigha ne ya ruwaito babban kwamandan su, inda ya kara da cewa Burgediya Janar din ya hori sojoji da su tabbatar da cewa a ko yaushe makaman su na samun kula ta wajen gyara da kuma yi musu garambawul.
Ya ce dalilin yi musu wannan gargadin shi ne domin su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, saboda a ko yaushe za a iya ba su umarnin su darkaki Boko Haram domin a yi ta ta kare.

Daga nan ya kuma tabbatar da cewa, wannan harin da za a kai, shi ne zai zama harin fatattakar Boko Haram kwata-kwata a kasar nan.

Share.

game da Author