Gwamnatin Jihar Bauchi za ta gina Dam 9

0

Kwamishinan ruwa na jihar Bauchi Mohammed Ghali, ya sanar cewa gwamnatin jihar ta gama shiri tsaf domin gina Dam guda 9 a Kafin Zaki, Karamar humar Ganjuwa, Dindimi karamar hukumar Alkaleri, Bagel/Zungur, Karamar hukumar Dass, Gambaki Karamar hukumar Katagum, Misau, Katini karamar hukumar Ningi, Gulka Giade, Tilden Fulani, karamar hukumar Toro da Boto dake karamar hukumar Tafawa Balewa.

Da yake ganawa da manema labarai, Ghali ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta kashe sama da nair biliyan 118 don wannan aiki.

Share.

game da Author