AMBALIYA: Gwamnatin tarayya ta samar da naira biliyan 1.5 wa jihohin 15

0

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina ya sanarwa manema labarai cewa gwamnati ta samar da naira biliyan 1.5 don raba wa jihohin da ambaliyar ruwa ya yi musu ta’adi.

Femi Adeshina ya ce jihohin da za su raba kudaden sun hada da Jihar Edo, Neja, Sokoto, Ekiti, Osun, Kwara, AkwaIbom, Kebbi, Bayelsa Ebonyi, Enugu, Abia Oyo Lagos da jihar Filato.

Ya kara da cewa tuni mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya umurci ministan Kudi da ta saki kudin. Ya ce gwamnati za ta yi amfani da kudaden da ke ajiye na ‘Ecological Fund’.

Za a ba hukumar ba da agajin gaggawa NEMA domin raba wa jihohin.

Share.

game da Author