Shugaban karamar hukumar Kauran Namoda Lawal Abdullahi ya sanar da kafa wata doka a karamar hukumar da ya hana siyar da giya, rufe gidajen wasannin caca da na kallo, da karuwanci a karamar hukumar.
Lawal ya ce karamar hukumar tayi haka ne ganin yadda lalacewa musamman ga matasa yak e kara yawa a garin.
Ya ce gwamnati ba za ta sa ido ta bari ba mutane na kauce hanya amma kuma basuyi komai akai ba.
Discussion about this post