Wasu kwararrun likitoci dake gudanar da bincike a kasar New Zealand na gab da samun alluran rigakafin cutar sanyi ‘Gonorrhoea’.
Shugaban masu binciken Helen Petousis ta ce a binciken da suka gudananr din sun gano cewa maganin cutar sankarau wato ‘Meningitis B’zai kare mutum daga kamuwa da wannan cutar sanyi din.
Ta ce binciken ya nuna cewa mutanen da suka yi wa allura da wannan magani na cutar sankarau din sun sami kariya kashi 30 bisa 100 daga kamuwa da ga cutar.
Helen Petousis ta ce duk da hakan har yanzu dai basu sami takamamman maganin da zai samar da kariya daga cutar sanyi na ‘Gonorrhoea’ ba amma suna ci gaba da bincike.
A makon da ya gabata ne Hukumar lafiya ta duniya WHO ta gargadi mutane da su yi kaffa-kaffa da kamuwa da cutar sanyi wato ‘Gonorrhoea’ domin yanzu fa bata jin magani.
Kungiyar WHO ta yi wannan shela ne don wayar da kan mutane sannan da tunashe su game da hadarin dake tattare da cutar musamman ganin maganinsa yayi wuya yanzu sannan kuma baya jin magani.
Ita dai wannan cutar sanyin da ake kira da ‘Gonorrhoea’ wata bacteria ce ke kawo ta mai suna ‘Neisseria gonorrhoeae ko kuma gonococcus’ wanda ke kama al’auran namiji ko mace.
Daya daga cikin alamonin cutar da ake iya gani idan an kamu shine yadda gaban namiji ko mace zai dunga fitar da farin ruwa wanda wata sa’an yakan yi wari sannan kuma an fi kamuwa da cutar ta hanyar saduwa da juna.
Kungiyar ta kuma gano a wani binciken da ta yi cewa a duk shekara mutane miliyan 78 na kamuwa da cutar; kasan Biritaniya kuwa ta ce kashi 10 bisa 100 sun kamu da cutar a shekaran 2015 sannan a kasar Faransa mutanen da ke aikata luwadi sun fi yawa cikin wadanda ke dauke da cutar a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015.
Kungiyar ta kara da cewa kasashen yankin Afrika sun fi yawa domin cikin mutane 10 mutum daya na dauke da cutar.
Kungiyar WHO ta bayyana wasu dalilan da ke kawo yaduwar cutar wanda ya hada da rashin amfani da kwarroro roba lokacin da za a yi jima’I da kuma rashin yin gwaji kan.