Wani dalibi da ke karatu a wata kwaleji a garin Lantang, jihar Filato ya rasa ransa sanadiyyar kamuwa da cutar lassa.
Bayan haka wasu dalibai biyu na samun kula a asibiti bayan an gano suna dauke da kwayoyin cutar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kuden Deyin a lokacin da yake tabbatar da hakan ya ce wasu daliban makarantar guda hudu ne a ka kai su Asibitin koyarwa na jami’ar Jos in da aka tabbatar da uku na dauke da cutar.
Ya shawarci mutane da su mai da hankalinsu wajen tsaftace muhallinsu da jikkunan su sannan kuma su nisantar da abincin su daaga kashi ko fitsarin bera domin shine ke kawo cutar.
Discussion about this post